1 Sai Joshuwa ɗan Nun ya aiki mutum biyu 'yan leƙen asirin ƙasa daga Shittim a asirce, ya ce musu, “Tafi, ku leƙo asirin ƙasar, musamman Yariko.” Suka tafi, suka shiga gidan wata mace, karuwa, sunanta Rahab, a nan suka sauka.
2 Sai aka faɗa wa Sarkin Yariko, aka ce, “Ga waɗansu mutane sun shigo nan da daddare domin su bincike ƙasar.”
3 Sarkin Yariko kuwa ya aika wurin Rahab ya ce, “Fito da mutanen da suka zo wurinki, waɗanda suka shiga gidanki, gama sun zo ne domin su leƙi asirin ƙasar duka.”
4 Amma macen ta riga ta ɓoye mutanen nan biyu, sai ta ce, “Gaskiya ce, mutanen sun zo wurina, amma ban san ko daga ina suka zo ba,
5 da maraice kuma, sa'ad da za a rufe ƙofar garin, sai mutanen suka fita, inda suka tafi kuwa ban sani ba, ku bi su da sauri, gama za ku ci musu.”