7 Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manassa gādo a Bashan, sauran rabin kabilar kuwa Joshuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu a yammacin hayin Urdun. Sa'ad da Joshuwa ya sallame su zuwa gida, ya sa musu albarka,
8 ya ce musu, “Ku koma gidajenku da wadata mai yawa, da dabbobi masu yawa, da azurfa, da zinariya, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da tufafi masu yawa. Ku raba da 'yan'uwanku ganimar da kuka kwaso daga abokan gabanku.”
9 Sai Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka koma gida. Suka yi bankwana da sauran 'yan'uwansu Isra'ilawa a Shilo ta ƙasar Kan'ana. Suka koma ƙasar Gileyad, ƙasar da suka gāda bisa ga umarnin Ubangiji ta bakin Musa.
10 Sa'ad da suka kai Gelilot, kusa da Urdun, a gefen da yake wajen ƙasar Kan'ana, suka gina babban bagade a wurin.
11 Sauran Isra'ilawa kuwa suka ji labari cewa, “Ga shi, Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa sun gina bagade a Gelilot a kan iyakar ƙasar Kan'ana, a wajen hayinsu na yammacin Urdun.”
12 Da Isra'ilawa suka ji haka sai dukansu suka tattaru a Shilo don su kai musu yaƙi.
13 Mutanen Isra'ila kuwa suka aiki Finehas, ɗan Ele'azara, firist, wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad.