31 Ya gina shi kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra'ilawa, gama haka aka rubuta cikin Attaura ta Musa, aka ce, “Bagaden da aka yi da duwatsun da ba a sassaƙa ba, waɗanda ba mutumin da ya taɓa sa musu guduma.” A bisansa suka miƙa hadayu ta ƙonawa ga Ubangiji, da hadayu na salama.