2 Ga Karin magana da za su taimake ka ka rarrabe da hikima, da kyakkyawar shawara, da fahimtar ma'anar zurfafan karin magana,
3 da yadda za ka karɓi koyarwa ta hanyar hikima, da adalci, da gaskiya, da sanin abin da yake daidai.
4 Sukan sa marar sani ya zama masani, sukan koya wa samari yadda za su zama masu amfani.
5 Waɗannan karin magana sukan ƙara wa masu ilimi hikima, sukan zama jagora ga masana,
6 don su fahimci ɓoyayyiyar ma'anar da take cikin karin magana, da mawuyatan al'amura waɗanda masu hikima suka ƙago.
7 In kana so ilimi dole ne ka fara da tsoron Ubangiji. Jahilai ba su san darajar hikima ba, sun kuwa ƙi su koya.
8 Ɗana, ka kasa kunne ga koyarwar mahaifinka, ka mai da hankali ga abin da mahaifiyarka take faɗa.