8 Akan kiyaye adali daga wahala, amma takan auko wa mugu.
9 Mutane sukan sha hasara ta wurin maganar marasa tsoron Allah, amma hikimar adalai takan yi ceto.
10 Birni yakan yi farin ciki saboda wadatar mutanen kirki, akwai kuma sowa ta farin ciki sa'ad da mugaye suka mutu.
11 Biranen da adalai suke cikinsu sukan ƙasaita, amma maganganun mugaye sukan hallakar da su.
12 Wauta ce a yi wa waɗansu maganar raini, amma mutum mai la'akari yakan kame bakinsa.
13 Ba wanda zai yarda ya faɗi asirinsa ga matsegunci, amma za ka amince wa amintaccen mutum.
14 Al'ummar da ba ta da masu ja mata gora, za ta fāɗi. Yawan mashawarta yake kawo zaman lafiya.