1 Mutumin da yake ƙaunar ilimi yakan so a faɗa masa kuskurensa, wauta ce mutum ya ƙi yarda a faɗa masa laifinsa.
2 Ubangiji yana murna da mutanen kirki, amma yakan hukunta masu shirya mugunta.
3 Mugunta ba ta kawo zaman lafiya, amma adalai sukan tsaya daram.
4 Matar kirki abar fāriya ce, abar murna ga mijinta, amma idan ta sa shi kunya, ta zama masa kamar ciwo a ƙashinsa.