1 Ɗa mai hikima yakan mai da hankali sa'ad da mahaifinsa yake kwaɓarsa, amma mutum mai girmankai ba ya yarda da kuskurensa.
2 Mutanen kirki za a sāka musu da alheri a kan abin da suke faɗa, amma mayaudara sukan ƙosa su ta da zaune tsaye.
3 Ka lura da irin abin da kake faɗa don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa.
4 Rago yakan ƙosa ya sami wani abu ainun, amma sam, ba zai samu ba. Mai mai da hankali ga aikinsa zai sami kowane abu da yake bukata.