11 Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, za ka rasa ta da sauri, amma wanda ya same ta da wahala, za ta yi ta ƙaruwa.
12 Idan ba bege, sai zuciya ta karai, amma muradin da ya tabbata zai cika ka da sa zuciya.
13 Idan ka ƙi shawara mai kyau wahala kake nemar wa kanka, idan ka bi ta kuwa za ka zauna lafiya.
14 Koyarwar masu hikima maɓuɓɓugar rai ce, za ta taimake ka ka kuɓuta sa'ad da ranka yake cikin hatsari.
15 Basira takan sa a girmama ka, amma mutanen da ba za a iya amincewa da su ba, a kan hanyar hallaka suke.
16 Mutum mai hankali a ko yaushe yakan yi tunani kafin ya aikata, amma wawa yakan tallata jahilcinsa.
17 Manzanni marasa aminci sukan haddasa wahala, amma waɗanda suke amintattu sukan kawo salama.