32 Muguntar mugun takan kawo hallakarsa, amma adalin mutum, an kiyaye shi ta wurin dattakonsa.
33 Hikima tana cikin kowane tunani na haziƙi, wawa bai san kome game da hikima ba.
34 Adalci yakan ɗaukaka al'umma, amma zunubi yakan kunyatar da al'umma.
35 Sarakuna suna jin daɗin ƙwararrun 'yan majalisarsu, amma sukan hukunta waɗanda suka ba su kunya.