3 Ubangiji yana ganin abin da yake faruwa a ko'ina, yana lura da mu, ko muna aikata alheri ko mugunta.
4 Kalmomin alheri suna kawo rai, amma maganganun ƙiyayya suna karya zuciyar mutum.
5 Wauta ce mutum ya ƙi kulawa da abin da mahaifinsa ya koya masa, amma hikima ce idan ka karɓi tsautawarsa.
6 Adalai suna adana dukiyarsu, amma mugaye sukan rasa tasu dukiya sa'ad da wahala ta zo.
7 Mutane masu hikima suke yaɗa ilimi, amma banda wawaye.
8 Ubangiji yana murna sa'ad da adalai suke yin addu'a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.
9 Ubangiji yana ƙin hanyoyin mugaye, amma yana ƙaunar mutumin da yake yin abin da yake daidai.