16 Yana da kyau, ya kuma fi kyau a sami hikima da ilimi fiye da zinariya da azurfa.
17 Mutumin kirki yana tafiya a hanyar da ta kauce wa mugunta, saboda haka ka kula da inda kake tafiya, za ta ceci ranka.
18 Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa.
19 Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu tawali'u, da ka zama ɗaya daga cikin masu girmankai, har da za ka sami rabo daga cikin ganimarsu.
20 Ka mai da hankali ga abin da aka koya maka, za ka yi nasara. Ka dogara ga Ubangiji, za ka yi farin ciki.
21 Mutum mai hikima, wanda ya isa mutum, akan san shi ta wurin haziƙancinsa, kamar yadda kalmominsa suke da daɗi, haka ma rinjayarsa take.
22 Hikima maɓuɓɓugar rai ce ga mai hikima, amma ɓata lokaci ne a yi ƙoƙarin koya wa dakikai.