1 Gara a ci ƙanzo da rai a kwance, da gida cike da liyafa, amma cike da tashin hankali.
2 Bara mai wayo yakan sami iko a kan shashashan ɗan maigidansa, har ya sami rabo a cikin gādon.
3 Zinariya da azurfa da wuta ake gwada su, zuciyar ɗan adam kuwa Ubangiji ne yake gwada ta.
4 Mugaye sukan kasa kunne ga mugayen dabaru, maƙaryata kuma sukan kasa kunne ga ƙarairayi.
5 Wanda ya yi wa matalauci ba'a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka.
6 Tsofaffi suna fāriya da jikokinsu, kamar yadda samari suke alfarma da iyayensu maza.