21 Abin da ka faɗa ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karɓi sakamakon maganarka.
22 Idan ka sami mace ka sami abu mai kyau, wannan alheri ne wanda Ubangiji ya yi maka.
23 Matalauci yakan yi roƙo da taushi, maganar matalauci rarrashi ne, amma attajiri yakan yi magana garas.
24 Waɗansu abokai ba su sukan ɗore ba, amma waɗansu abokai sun fi 'yan'uwa aminci.