1 Sa'ad da ka zauna cin abinci tare da babban mutum, ka tuna da yadda yake.
2 Idan kai mai son ci da yawa ne sai ka kanne.
3 Kada ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da yake gabanku, zai yiwu wayo yake so ya yi maka.
4 Ka zama mai isasshiyar hikima, kada ka gajiyar da kanka garin ƙoƙarin neman dukiya.
5 Kuɗinka sun iya ƙarewa kamar ƙyiftawar ido, kamar suna da fikafikai su tashi kamar gaggafa.