8 Idan a ko yaushe shirye-shiryen mugunta kake, za ka yi suna a kan kuta tashin hankali.
9 Kowace irin dabarar da wawa yake tunani a kanta zunubi ne. Jama'a suna ƙin mutum mai rainako.
10 Idan ba ka da ƙarfi a lokacin hargitsi, hakika ka tabbata marar ƙarfi.
11 Kada ka ji nauyin ceton wanda ake janye da shi zuwa inda za a kashe shi.
12 Mai yiwuwa ne ka ce kai ba ruwanka, amma Allah ya sani, yana kuwa auna manufofinka. Yana lura da kai, ya kuwa sani. Yakan sāka wa mutane a kan abin da suke aikatawa.
13 Ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau. Kamar yadda kakin zuma yake da zaƙi a harshenka,
14 haka ilimi da hikima suke da amfani ga ranka. Ka same su, a gaba za ka yi farin ciki.