1 Ga waɗansu sauran karin maganar Sulemanu waɗanda magatakardan Hezekiya Sarkin Yahuza suka juya.
2 Muna girmama Allah saboda abin da ya rufe, muna girmama sarakuna saboda abin da suka ba da bayaninsa.
3 Ba ku taɓa sanin abin da sarki yake tunani ba, gama tunaninsa sun fi ƙarfinmu. Kamar nisan sararin sama suke ko zurfafan teku.
4 Ka tace azurfa, gwani kuwa zai yi wani kyakkyawan abu da ita.
5 A kawar da mugayen mashawarta daga gaban sarki, hukumarsa za ta shahara a kan adalci.
6 Sa'ad da kake tsaye a gaban sarki, kada ka nuna kai wani abu ne, kana kai kanka inda Allah bai kai ka ba.
7 Gara a roƙe ka ka hau zuwa babban matsayi, da a faɗa maka ka ba da wurin da kake ga wanda ya fi ka maƙami.