18 Mutumin da yakan faɗi ƙarairayi a kan maƙwabcinsa, shi kamar kakkaifan takobi ne, ko kulki, ko kibiya mai tsini.
19 Dogara ga marar aminci a lokacin hargitsi, kamar ƙoƙarin yin tauna da ruɓaɓɓun haƙora ne, ko yin tafiya da mai gurguwar ƙafa,
20 ko kuma ka yi ƙoƙarin jin ɗumi ta wurin tuɓe tufafinka a ranar da ake sanyi.Raira waƙa ga mai baƙin ciki kamar marmasa gishiri a kan rauni ne.
21 Idan maƙiyinka yana jin yunwa ka cishe shi, idan yana jin ƙishi ka ba shi abin sha.
22 Za ka sa ya sha kunya, Ubangiji kuma zai sāka maka.
23 Iskar arewa takan kawo ruwan sama, haka kuma jita-jita takan kawo fushi.
24 Gara zama a saƙo da zama a gida ɗaya tare da mata mai mita.