1 Yabo bai dace da wawa ba, kamar yadda dusar ƙanƙara ba ta dace da lokacin zafi ba, ko ruwan sama a lokacin girbi.
2 La'ana ba za ta kama ka ba, sai dai in ka cancance ta. Tana kamar tsuntsayen da suke firiya da dare ba za su sauka ba.
3 Sai ka fyaɗi doki, ka sa wa jaki linzami, wawa kuma sai ka doke shi.
4 Idan ka amsa tambayar wauta, ka zama wawa daidai da mutumin da ya yi tambayar.
5 Ka amsa wauta ga tambayar wauta, wanda ya yi tambayar zai gane wawancinsa.
6 Mutumin da ya sa wawa ya isar masa da saƙo ya datse ƙafafunsa, yana nemar wa kansa wahala.
7 Wawa yakan yi amfani da karin magana kamar yadda tauyayyen mutum yake amfani da ƙafafunsa.