13 Ka karɓe tufar wanda ya zamar wa baƙo lamuni, da kuma wanda ya zama lamunin karuwa.
14 In ka farkar da abokinka da babbar murya tun da sassafe, daidai ne da zaginsa.
15 Mace mai mita kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa.
16 Kaƙa za ka iya sa ta ta kame bakinta? Ka taɓa ƙoƙarin tsai da iska? Ko kuwa ka taɓa ƙoƙarin dintsi mai a tafin hannunka?
17 Daga wurin mutane mutane suke koyo, kamar yadda a kan wasa ƙarfe da ƙarfe.
18 Ka lura da itacen ɓaure, zai yi 'ya'ya ka ci. Baran da ya lura da maigidansa za a girmama shi.
19 Yadda kake ganin fuskarka a ruwa, haka kake ganin kanka a zuciyarka.