23 Ka lura da garkunan tumakinka da na shanunka da kyau iyakar iyawarka,
24 domin dukiya ba ta tabbata har abada, al'ummai ma haka ne.
25 Ka yanki ingirici, lokacin da yake toho kana iya yankar ciyawa a gefen tuddai.
26 Kana iya yin tufafi da ulun tumakinka, kana iya sayen gona da kuɗin awakinka.
27 Madarar awakinka za ta zama abincinka kai da iyalinka, da kuma barorinka 'yan mata.