1 Mugun mutum yakan gudu, alhali kuwa ba mai korarsa, amma amintaccen mutum kamar zaki yake, ba shi da tsoro.
2 Al'umma za ta ƙarfafa ta jure idan shugabanninta masu basira ne, masu hankali. Amma idan ƙasar mai aikata zunubi ce za ta sami shugabanni da yawa.
3 Mai mulki wanda yake zaluntar talakawa, ya zama kamar ruwa mai lalatar da amfanin gona.
4 Wanda ba ya bin doka tare da mugaye yake, amma idan kana bin doka kai abokin gāban mugaye ne.
5 Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada sun san ta sosai.
6 Gara ka zama matalauci mai aminci da ka zama mawadaci, marar aminci.
7 Saurayi wanda ya kiyaye doka mai basira ne shi, amma wanda yake abuta da 'yan iska zai zama mai jawo wa mahaifinsa kunya.