23 Za ka bi hanyarka lafiya lau, ba ko tuntuɓe.
24 Ba za ka ji tsoro, sa'ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare.
25 Ba za ka damu da masifar da za ta auko farat ɗaya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri.
26 Ubangiji zai kiyaye ka. Ba zai bari ka fāɗa cikin tarko ba.
27 Ka yi wa masu bukata alheri a duk lokacin da kake iyawa.
28 Sam, kada ka ce wa maƙwabcinka ya dakata sai gobe, idan dai kana iya taimakonsa yanzu.
29 Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, gama yana zaune kusa da kai, yana kuwa amincewa da kai.