1 'Ya'yana ku kasa kunne ga koyarwar mahaifinku. Ku mai da hankali, za ku zama haziƙai.
2 Abin da nake koya muku, abu mai kyau ne, saboda haka ku tuna da shi duka.
3 Sa'ad da nake ɗan yaro tilo a wurin iyayena,
4 mahaifina yakan koya mini, yakan ce, “Ka tuna da abin da nake faɗa maka, kada ka manta. Ka yi abin da na faɗa maka za ka rayu.
5 Ka nemi hikima da basira! Kada ka manta ko ka ƙyale abin da na faɗa.
6 Kada ka rabu da hikima, gama za ta kiyaye ka, ka ƙaunace ta, za ta kiyaye lafiyarka.