1 Ɗana, ka mai da hankali, ka kasa kunne ga hikimata da basirata.
2 Sa'an nan ne za ka san yadda za ka yi kome daidai, kalmominka za su nuna kana da ilimi.
3 Leɓunan matar wani, mai yiwuwa ne, su yi zaƙi kamar zuma, sumbace-sumbacenta kuma su fi man zaitun taushi.
4 Amma bayan an gama duka, ba abin da za ta bar maka sai baƙin ciki, da azaba.
5 Za ta gangara da kai zuwa lahira, hanyar da take bi hanyar mutuwa ce.
6 Ba a kan hanyar rai take ba, tana ragaita nesa da hanyar, amma kai ba ka ankara ba.
7 'Ya'yana, ku kasa kunne gare ni yanzu, kada ko kusa ku manta da abin da nake faɗa.