11 Amma lokacin da yake sharar barci, tsiya za ta auka masa kamar ɗan fashi da makamai.
12 Sakarkari, wato mugaye sukan yi ta baza jita-jita.
13 Sukan yi ƙyifce, ko su yi nuni don su yaudare ka.
14 A kowane lokaci suna shirya mugunta a kangararren hankalinsu, suna kuta tashin hankali ko'ina.
15 Saboda wannan masifa za ta fāɗa musu farat ɗaya ba makawa, za a yi musu mummunan raini.
16-19 Akwai abu shida, i, har bakwai ma, waɗanda Ubangiji yake ƙi, waɗanda ba zai haƙura da su ba,duban raini,harshe mai faɗar ƙarya,hannuwan da suke kashe marasa laifi,kwanyar da take tunane-tunanen mugayen dabaru,mutum mai gaggawar aikata mugunta,mai yawan shaidar zur,mutum mai ta da fitina a tsakanin abokai.
20 Ɗana, ka yi abin da mahaifinka ya faɗa maka, kada ka manta da koyarwar mahaifiyarka.