15 Saboda wannan masifa za ta fāɗa musu farat ɗaya ba makawa, za a yi musu mummunan raini.
16-19 Akwai abu shida, i, har bakwai ma, waɗanda Ubangiji yake ƙi, waɗanda ba zai haƙura da su ba,duban raini,harshe mai faɗar ƙarya,hannuwan da suke kashe marasa laifi,kwanyar da take tunane-tunanen mugayen dabaru,mutum mai gaggawar aikata mugunta,mai yawan shaidar zur,mutum mai ta da fitina a tsakanin abokai.
20 Ɗana, ka yi abin da mahaifinka ya faɗa maka, kada ka manta da koyarwar mahaifiyarka.
21 Kullum ka kiyaye abin da suke faɗa maka, ka kulle su kuma a zuciyarka.
22 Koyarwarsu za ta bi da kai sa'ad da kake tafiya, ta kiyaye ka da dare, ta kuma ba ka shawara da rana.
23 Doka da abubuwan da take koyarwa haske ne mai haskakawa. Tsautawa tana iya koya maka zaman duniya.
24 Za ta tsare ka daga mugayen mata, daga kalmomin alfasha da suke fitowa daga bakin matan waɗansu.