1 Ɗana, ka tuna da abin da na faɗa, kada ka manta da abin da na ce maka ka yi.
2 Ka yi abin da na faɗa maka, za ka rayu. Ka natsu, ka bi koyarwata, ka tsare ta kamar ƙwayar idonka.
3 Kullayaumi ka riƙe koyarwata tare da kai, ka rubuta ta a zuciyarka.
4 Ka mai da hikima 'yar'uwarka, basira kuwa ta zama ƙawarka ta jikinka.
5 Za su nisanta ka da matan mutane, daga kuma mata masu maganganun alfasha.