33 Ku saurari abin da aka koya muku,Ku zama masu hikima, kada ku yi sakaci da ita.
34 Mutumin da ya kasa kunne gare ni, zai yi farin ciki haka nan,Wato yakan tsaya a ƙofata ko yaushe,Yana kuma jira a ƙofar shiga gidana.
35 Mutumin da ya same ni ya sami rai,Ubangiji zai ji daɗinsa.
36 Mutumin da bai same ni ba ya cuci kansa,Duk wanda yake ƙina mutuwa yake ƙauna.”