1 Hikima ta gina gidanta, ta yi masa ginshiƙai bakwai.
2 Ta sa an yanka dabba don biki, ta gauraya ruwan inabi da kayan yaji, ta shirya tebur.
3 Ta aiki barorinta 'yan mata su je su hau wuri mafi tsayi a birni su yi kira.
4 “Ku shigo, ku jahilai!” Ga dolo kuwa ta ce,
5 “Zo ka ci abincina ka sha ruwan inabin da na gauraya.
6 Ka rabu da ƙungiyar jahilai, ka rayu, ka bi hanyar ilimi.”
7 Idan ka kwaɓi mai fāriya, za ka gamu da cin mutunci, idan ka tsauta wa mugu, kai ne za ka cutu.