1 Ubangiji ya kirawo Musa, ya yi masa magana daga cikin alfarwa ta sujada, ya ce
2 ya ba Isra'ilawa ka'idodin nan.Sa'ad da kowane mutum a cikinsu zai kawo sadaka ga Ubangiji, sai ya kawo sadakarsa daga cikin garkunansa na shanu, da na tumaki, da na awaki.
3 Idan sadakarsa ta hadayar ƙonawa ce daga cikin garken shanu, sai ya ba da namiji marar lahani, zai miƙa shi a ƙofar alfarwa ta sujada domin sadakar ta zama abar karɓa a gaban Ubangiji.
4 Sai ya ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya ta ƙonawar, za a karɓa masa, a kuwa yi masa gafara.
5 Sa'an nan zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna maza, firistoci, za su miƙa jinin a bagaden da yake a ƙofar alfarwa ta sujada za su kuma yayyafa jinin a kewaye da shi.
6 Sai mai hadayar ya feɗe dabbar, ya yanyanka ta gunduwa-gunduwa.