1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi
2 domin Isra'ilawa. Za ku ci kowace irin dabbar da take a duniya,
3 wadda take da rababben kofato, wadda kuma take yin tuƙa.
4 Ko daga cikin masu tuƙar ko masu rababben kofaton ba za ku ci waɗannan ba. Raƙumi yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku.
5 Rema tana tuƙa, amma ba ta da rababben kofato, haram ce a gare ku.