41 ya sa a kankare jikin gidan duka. Shafen da suka kankare kuwa, sai su zubar da shi a wuri marar tsarki can bayan birnin.
42 Sa'an nan sai su kwaso waɗansu duwatsu, su sa su a wuraren da suka ciccire waɗancan. Sai a kawo laka a shafe gidan.
43 Idan cutar ta sāke ɓulla a cikin gidan bayan da aka ciccire duwatsun, aka kuma kankare gidan, aka yi masa shafe,
44 sai firist ya je ya duba, idan cutar ya yaɗu a gidan, to, muguwar kuturta ce, gidan marar tsarki ne.
45 Sai a rushe gidan, a kwashe duwatsun gidan, da katakansa, da shafensa duka a zubar bayan birni a wuri marar tsarki.
46 Duk wanda ya shiga gidan bayan da an rufe shi, zai ƙazantu har maraice.
47 Wanda kuma ya kwana cikin gidan, sai ya wanke tufafinsa, haka kuma wanda ya ci abinci cikin gidan, zai wanke tufafinsa.