1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi
2 domin jama'ar Isra'ila. Duk lokacin da wani namiji yake ɗiga daga al'aurarsa, ƙazantacce ne.
3 Ko al'aurar tana ɗiga ko ta daina shi dai ƙazantacce ne.
4 Kowane gado da mai ɗigan ya kwanta a kai ya ƙazantu, da kowane abu da ya zauna a kai ya ƙazantu.
5 Duk wanda ya taɓa gadonsa, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.
6 Duk wanda kuma ya zauna a kan kowane abin da mai ɗigar ya zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.