15 Kada ya kwana da matar ɗansa, gama ita surukarsa ce.
16 Kada ya kwana da matar ɗan'uwansa, gama ita matar ɗan'uwansa ce.
17 In ya kwana da mace, kada kuma ya kwana da 'yarta, ko jikanyarta, wannan duk haramun ne, gama su danginsa ne na kusa.
18 Muddin matarsa tana da rai, ba zai auro ƙanwarta ta zama kishiyarta ba.
19 Kada ya kwana da mace a lokacin hailarta, gama ba ta da tsarki.
20 Kada ya kwana da matar maƙwabcinsa don kada ya ƙazantar da kansa.
21 Kada ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa don a miƙa wa Molek, gama yin haka zai ƙasƙantar da sunan Allah. Shi Ubangiji ne.