3 Kada ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan'ana inda nake kai ku. Kada ku kiyaye dokokinsu.
4 Amma ku bi ka'idodina, ku yi tafiya a cikinsu, gama ni ne Ubangiji Allahnku.
5 Domin haka sai ku kiyaye dokokina da ka'idodina waɗanda ta wurin kiyaye su mutum zai rayu. Ni ne Ubangiji.”
6 Ubangiji ya ba da waɗannan ka'idodi kuma. Kada kowane mutum ya kusaci 'yar'uwarsa don ya kwana da ita. Ya ce, “Ni ne Ubangiji.”
7 Kada ya ƙasƙantar da mahaifinsa, wato, kada ya kwana da mahaifiyarsa, kada ya ƙasƙantar da mahaifiyarsa.
8 Kada ya kwana da matar mahaifinsa, gama ita matar mahaifinsa ce.
9 Kada ya kwana da 'yar'uwarsa, 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa, ko a gida ɗaya aka haife ta da shi, ko a wani gida dabam.