29 “Kada ku ƙasƙantar da 'ya'yanku mata ta wurin sa su su zama karuwan masujadai, idan kuka yi haka, za ku juya ga gumaka, ƙasar za ta cika da lalata.
30 Sai ku kiyaye lokatan sujada, ku kuma darajanta alfarwata mai tsarki. Ni ne Ubangiji.
31 “Kada ku tafi wurin masu mabiya, kada kuma ku nemi shawarar bokaye, domin kada su sa ku ku ƙazantu. Ni ne Ubangiji Allahnku.
32 “Ku girmama tsofaffi ku darajanta su, gama kuna tsorona. Ni ne Ubangiji.
33 “Idan baƙo ya baƙunce ku a ƙasarku, kada ku cuce shi.
34 Amma ku ɗauke shi tankar ɗan ƙasa, ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
35 “Kada ku cuci wani wajen yin amfani da kowane irin ma'auni na ƙarya, wato, awon tsawo, ko na nauyi, ko na ruwa.