1 A sa'ad da mutum ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, sai ya kawo gari mai laushi, ya zuba masa mai da lubban.
2 Zai kuma kawo hadayarsa a wurin 'ya'yan Haruna maza, firistoci. Zai ɗibi tāfi guda na lallausan garin da aka zuba wa mai da dukan lubban. Firist kuwa zai ƙona wannan a kan bagaden don tunawa, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
3 Ragowar garin hadayar kuwa, zai zama na Haruna da 'ya'yansa maza, gama hadaya ce ta ƙonawa mafi tsarki ga Ubangiji.
4 Sa'ad da aka kawo hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, sai a yi shi da gari mai laushi marar yisti kwaɓaɓɓe da mai, a shafa masa mai, a toya, ko kuwa a soya ƙosai.
5 Idan kuwa hadayar ta gari ce da aka toya cikin kaskon tuya, sai a yi abinci da gari mai laushi wanda ba a sa masa yisti ba, wanda aka kwaɓa da mai.
6 Za a gutsuttsura shi, a zuba masa mai, hadayar gari ke nan.