17 “Idan mutum ya auri ƙanwarsa ko kuma 'yar mahaifinsa, sai a ƙasƙantar da su a bainar jama'a, a kuwa kore su daga cikin jama'a. Ya kwana da ƙanwarsa ke nan, tilas su sha hukuncin laifinsu.
18 Idan mutum ya kwana da mace a lokacin hailarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama'arsu, gama sun karya ka'idodi a kan rashi tsarki.
19 “Idan mutum ya kwana da bābarsa ko innarsa, za a hukunta duka biyunsu saboda abin ƙyama da suka yi.
20 Idan kuma mutum ya kwana da matar kawunsa, ya ƙasƙantar da kawunsa, sai su ɗauki alhakin laifinsu, za su mutu ba haihuwa.
21 Idan mutum ya auri matar ɗan'uwansa, ya yi mugun abu, za su mutu ba haihuwa, gama ya ƙasƙantar da ɗan'uwansa.
22 “Sai fa ku kiyaye dokokina duka, da ka'idodina duka, ku kuma aikata su domin kada ƙasar da nake kai ku ta amayar da ku.
23 Kada ku bi al'adun waɗannan al'ummai, waɗanda nake kora a gabanku, gama sun aikata waɗannan al'amura, don haka nake ƙyamarsu.