1 Ubangiji kuma ya umarce Musa, ya faɗa wa 'ya'yan Haruna, maza, firistoci cewa, “Kada ko wannensu ya ƙazantar da kansa ta wurin gawar mutanensa,
2 sai dai gawar iyalinsa na kurkusa, wato, gawar mahaifiyarsa, da ta mahaifinsa, da ta ɗansa, da ta 'yarsa, da ta ɗan'uwansa,
3 da ta 'yar'uwarsa, budurwa, da take kusa da shi, wadda ba ta yi aure ba tukuna. Saboda su ya iya ƙazantar da kansa.
4 Kada ya ƙazantar da kansa saboda dangantakar aure cikin mutanensa.