1 Ubangiji kuma ya umarci Musa
2 ya faɗa wa Haruna, da shi da 'ya'yansa cewa, “Ku lura da tsarkakakkun abubuwa waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, don kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Ni ne Ubangiji.
3 Idan kowanne daga cikin dukan zuriyarku ya kusaci tsarkakakkun abubuwa, waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, lokacin da yake ƙazantacce, wannan mutum ba zai ƙara kasancewa a gabana ba, wannan kuwa zai zama har dukan lokatai masu zuwa. Ni ne Ubangiji.
4 “Daga cikin zuriyar Haruna wanda yake kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,