26 Ubangiji ya yi magana da Musa, ya ce,
27 “Sa'ad da kuma aka haifi ɗan maraƙi, ko ɗan rago, ko ɗan akuya, zai yi kwana bakwai tare da uwarsa. A rana ta takwas zuwa gaba, sai a karɓe shi don yin hadaya ta ƙonewa ga Ubangiji.
28 Ba za ku yanka uwar dabbar tare da ɗanta rana ɗaya ba, ko uwar saniya ce, ko ta tunkiya ce.
29 Sa'ad da za ku miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, sai ku miƙa ta yadda za a karɓa.
30 A ranar ce za a cinye, kada a bar kome ya kai gobe. Ni ne Ubangiji.
31 “Ku yi biyayya da umarnina. Ni ne Ubangiji.
32 Kada ku jawo wa sunana mai tsarki ƙasƙanci, amma sai mutanen Isra'ila su gane, ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji na kuwa tsarkake ku,