1 Ubangiji ya ba Musa
2 waɗannan ka'idodi domin ƙayyadaddun idodi sa'a da Isra'ilawa za su taru domin yin sujada.
3 Cikin kwanaki shida za a yi aiki, amma a rana ta bakwai za a huta ɗungum, gama ranar Asabar ce, tsattsarka. Ko kaɗan ba za a yi aiki a ranar ba a duk inda suke, amma ku yi taruwa ta sujada gama ranar Asabar ta Ubangiji ce.
4 Su yi waɗannan idodi a ƙayyadaddun lokatai.