29 Duk wanda ya ci abinci a wannan rana ba za a lasafta shi ɗaya daga cikin jama'ar Allah ba.
30 Duk kuma wanda ya yi aiki a wannan rana, Ubangiji kansa zai kashe shi.
31 Wannan ka'ida ta shafi dukan zuriyarsu a duk inda suke.
32 Daga faɗuwar ranar tara ga watan, har zuwa faɗuwar ranar goma ga watan, su kiyaye wannan ta zama ranar hutu musamman. A wannan lokaci ba wanda zai ci abinci.
33 Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce ya faɗa wa Isra'ilawa, cewa,
34 a rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi Idin Bukkoki kwana bakwai saboda Ubangiji.
35 Za a yi muhimmin taro na sujada a rana ta fari. Ba za su yi aiki ba.