18 “Domin haka sai ku kiyaye farillaina, da ka'idodina. Ku aikata su domin ku zauna a ƙasar lami lafiya.
19 Ƙasar za ta ba da amfani, za ku ci, ku ƙoshi, ku zauna lafiya.
20 “Idan kuwa kun tambaya abin da za ku ci a shekara ta bakwai, idan ba za ku yi shuka ba, ba kuwa za ku tattara amfanin gona ba,
21 ku sani zan sa muku albarka a shekara ta shida don ta ba da isasshen amfanin da zai kai ku shekara uku.
22 Sa'ad da za ku yi shuka a shekara ta takwas, shi ne za ku yi ta ci, har shekara ta tara lokacin da za ku yi girbi.”
23 “Kada a sayar da gona din din din, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi na da kuke baƙunci a wurina.
24 “Amma kuna iya jinginar da gonar da kuka mallaka.