9 A ranar kafara, goma ga wata na bakwai za su busa ƙahon rago da ƙarfi cikin ƙasarsu duka.
10 Shekara ta hamsin kuwa za su keɓe ta, su yi shelar 'yanci cikin ƙasar duka ga dukan mazaunanta. Za ta zama shekarar murna a gare su. Kowa zai koma mahallinsa, ko wannensu kuma wurin danginsa.
11 Shekarar nan ta hamsin za ta zama shekara ta murna a gare su. A cikinta ba za su yi shuka, ko su girbe gyauro ba, ba kuwa za su tattara 'ya'yan inabin da ba su yi wa aski ba.
12 Shekara ce ta murna, za ta zama keɓaɓɓiya a gare su. Za su ci albarkar da gonakin suka bayar.
13 Ubangiji ya ce, “A wannan shekara ta hamsin ta murna kowa zai koma mahallinsa.
14 In ka sayar, ko ka sayi gona a wurin ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, kada ku cuci juna.
15 Idan za ka yi sayayya a wurin maƙwabcinka, sai ka lura da yawan shekarun da za ka mora kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo.