1 Ubangiji ya ce, “Kada ku yi wa kanku gumaka, ko ku kafa sassaƙaƙƙiyar siffa, ko al'amudi. Kada kuma ku kafa wata siffa ta dutse a ƙasarku da za ku durƙusa mata, gama ni ne Ubangiji Allahnku.
2 Sai ku kiyaye lokatan sujadata, ku girmama alfarwa ta sujada. Ni ne Ubangiji.
3 “Idan kun bi dokokina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su,
4 sa'an nan zan ba da ruwan sama a lokacinsa, ƙasar kuwa za ta ba da albarkarta, itatuwan gonaki kuma za su ba da 'ya'yansu.