10 Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin ya ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya.
11 Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da tarosonsa,
12 da sauran bijimin duka zai kai su waje bayan zango a wuri mai tsabta inda ake zubar da toka, nan zai ƙone su da wuta a inda ake zubar da tokar.
13 Idan taron jama'ar Isra'ila sun yi zunubi, ba da gangan ba, har sun aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, amma ba su farga da laifinsu ba, duk da haka sun yi laifi.
14 Amma sa'ad da zunubin da suka aikata ya sanu, taron jama'a za su ba da ɗan bijimi na yin hadaya don zunubi. Za a kawo shi a gaban alfarwa ta sujada.
15 Sai dattawan jama'a su ɗibiya hannunsu a kan kan bijimin a gaban Ubangiji, sa'an nan a yanka bijimin a gaban Ubangiji.
16 Sai keɓaɓɓen firist ya ɗibi jinin bijimin, ya kai cikin alfarwa ta sujada.