10 Firist zai sa rigarsa ta lilin, ya ɗaura mukurunsa na lilin, sa'an nan ya kwashe tokar hadaya ta ƙonawa daga bagaden, ya zuba a gefensa.
11 Firist ɗin kuma zai tuɓe rigunansa, ya sa waɗansu, sa'an nan ya kwashe tokar ya kai bayan zango ya zuba a wani wuri mai tsabta.
12 Sai a bar wutar bagaden ta yi ta ci, kada a kashe ta. Firist ɗin ya yi ta iza wutar kowace safiya, ya shimfiɗa hadaya ta ƙonawa a jere a bisa wutar, ya kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a bisanta.
13 Sai wuta ta yi ta ci a bisa bagaden kullum, kada ta mutu.
14 Wannan ita ce dokar hadaya ta gari. 'Ya'yan Haruna, maza, za su miƙata a gaban Ubangiji daga gaban bagaden.
15 Ɗaya daga cikinsu zai ɗibi lallausan garin hadayar wanda aka zuba masa mai da lubban cike da tafin hannunsa. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa.
16 Haruna da 'ya'yansa maza za su ci ragowar garin. Za a ci shi ba tare da yisti ba a wuri mai tsarki na farfajiyar alfarwa ta sujada.