9 ya ba Haruna da 'ya'yansa maza ka'idodin hadayu na ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za ta kwana bisa bagaden, wutar bagaden kuma ta kwana tana ci har safe.
10 Firist zai sa rigarsa ta lilin, ya ɗaura mukurunsa na lilin, sa'an nan ya kwashe tokar hadaya ta ƙonawa daga bagaden, ya zuba a gefensa.
11 Firist ɗin kuma zai tuɓe rigunansa, ya sa waɗansu, sa'an nan ya kwashe tokar ya kai bayan zango ya zuba a wani wuri mai tsabta.
12 Sai a bar wutar bagaden ta yi ta ci, kada a kashe ta. Firist ɗin ya yi ta iza wutar kowace safiya, ya shimfiɗa hadaya ta ƙonawa a jere a bisa wutar, ya kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a bisanta.
13 Sai wuta ta yi ta ci a bisa bagaden kullum, kada ta mutu.
14 Wannan ita ce dokar hadaya ta gari. 'Ya'yan Haruna, maza, za su miƙata a gaban Ubangiji daga gaban bagaden.
15 Ɗaya daga cikinsu zai ɗibi lallausan garin hadayar wanda aka zuba masa mai da lubban cike da tafin hannunsa. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa.