26 Ko kaɗan, ba za a yi abinci da jini ba, ko na tsuntsu, ko na dabba, a inda suke duka.
27 Duk mutumin da ya karya wannan doka za a raba shi da mutanensa.
28 Ubangiji kuma ya ba Musa waɗannan ka'idodi
29 don mutanen Isra'ila, cewa, wanda zai miƙa hadayarsa ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama.
30 Sai shi kansa ya kawo hadayar da za a ƙona. Zai kawo kitsen da ƙirjin. Za a yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin a gaban Ubangiji.
31 Firist zai ƙone kitsen a bisa bagaden, amma ƙirjin zai zama rabon Haruna da 'ya'yansa maza.
32 Za a ba firist cinya ta dama, don hadaya ta ɗagawa daga cikin hadayu na salama.